Mutane Da Dama Sun Hallaka Sanadiyar Ruwan Sama A Indiya.
Sama da mutane 100 suka mutu kana wasu 143 suka jikkata a sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka sheka a arewacin kasar Indiya daga daran Larba zuwa Alhamis
Kamfanin dillancin Labaran Irna na kasar Iran ya nahalto hukumomin kasar Indiyan na cewa ambaliyar ruwan ya fi shafar Jihohin Uttar Pradesh da Rajasthan dake arewacin kasar inda aka samu asarar rayuka sossai, sannan sun ce addadin wadanda suka mutun zai iya karuwa a cikin awowi na gaba masu zuwa.
Sanarwar ta ce yawancin wadanda suka mutun gine-gine ne suka ruguza da su, saboda karfin ruwan saman dake tare da iska mai karfi .
Har ila yau wannan lamari ya yi sanadiyar yankewar wutar lantarki a yankuna masu yawa na arewacin kasar.