Farashin Danyan Man Ya Tashi A Duniya
Zuwa karshen mu'amalar cinikayar da aka yi na jiya juma'a, farashin danyan man fetir ya tashi daga dala 69 zuwa 72 a Duniya
Kamfanin dillancin labaran Reuteus ya habarta cewa , a karshen mu'amalar cinikayar da aka yi na yammacin jiya juma'a, farashin danyan man ya tashi daga dala 69 zuwa dala 72.
A cewar manasa, tashin farashin danyan mai din ba ya rasa nasaba da kusantowar ranar 12 ga watan Mayu, inda a wannan rana ce ake zaton cewa shugaba Trump na Amurka zai bayyana matsayarsa na ficewa ko zama a yarjejjeniyar da kasar Iran ta kulla da manyan kasashen Duniya 5 da kasar Jamus a game da shirin nukiyarta na zaman lafiya.
Ko baya ga hakan, a ranar 30 Nuwambar 2016, kungiyar OPEC ta amince da rage yawan Man da take hakowa, sannan a karshen wannan shekara kasar Rasha da wasu kasashe 9 na daban sun amince da wannan kudiri.