Faransa : Ana Ci Gaba Da Zanga-Zangar Kyamar Macron
(last modified Sat, 05 May 2018 17:28:53 GMT )
May 05, 2018 17:28 UTC
  • Faransa : Ana Ci Gaba Da Zanga-Zangar Kyamar Macron

A Faransa dubban mutane ne suka fito wata zanga-zanga a wasu sassan kasar ciki har Paris don nuna rashin amincewa da manufofin shugaban kasar Emanuelle Macron.

Rahotannin daga kasar sun ce zanga zangar ta fi karbuwa a Paris babban birin kasar, inda 'yan sanda suka ce mutanen da suka halarci zanga zangar su kai 40,000 ko da yake wadanda suka shirya zanga zangar sun ce mutanen su haura 160,000 .

Wasu rahotannin na daban na cewa duk da dimbin jami’an tsaron da aka jibge, musamman a wajajen Cibiyar Central Opera Square, hakan bai hana masu zanga-zangar haduwa ba. 

An kuma yi irin wannan zanga zangar a biranen Toulouse da Boreaux, amma ta birnin Paris ta fi karbuwa, inda har ma aka samu fashe fashe shaguna.

A baya bayan nan dai Shugaban kasar ta Faransa, Emanuelle Macron na shan suka kan wasu manufofinsa daga wajen 'yan kasar.