Martanin Duniya kan Janyewar Amurka Daga Yarjejeniyar Nukiliyar Iran
(last modified Wed, 09 May 2018 08:47:56 GMT )
May 09, 2018 08:47 UTC
  • Martanin Duniya kan Janyewar Amurka Daga Yarjejeniyar Nukiliyar Iran

Tun bayan da shugaba Donald Trump na Amurka ya sanar da janye kasarsa daga yarjejeniyar nukiliyar da manyan kasashen duniya suka cimma da Jamhuriya Musulinci ta Iran, duniya ke ci gaba da maida martani kan matakin na Trump.

A jiya Talata ne dai Mista Trump ya sanar cewa, kasarsa za ta janye jiki daga yarjejeniyar nukiliyar kasar Iran, inda a cikin jawabinsa a fadar White House, Trump ya ce, yarjejejniyar nukiliyar Iran ba ta dace sam ba, Kana kasarsa za ta sake sanya takunkumi kan Iran.

Matakin na trump dai ya ci karo da martani daga kusuryoyi daban daban na duniya.

Kasashen Faransa, Jamus da Biritaniya sun yi nadamar matakin na Trump, a cewar shugaban kasar Faransa Emanuelle Macron a shafinsa na Twitter.

A wata sanarwa ta hadin gwiwa da suka fitar, shugaban kasar Faranasa Emanuelle Macron da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da firaministar Biritaniya Theresa May, wadanda suka yi ta rokon Trump da kada ya jenya daga yarjejeniyar sun ce zasu ci gaba da mutunta yarjejeniyar ta hanyar aiki da ita.

Ita ma kasar Rasha a nata bangare ta nuna matukar jin takaici da matakin na Trump.

Shi ma dai tsohon shugaban kasar ta Amurka, Barack Obama, wanda aka cimma yarjejeniyar a watan Yuli na 2015 a karkashin gwamnatinsa, ya bayana matakin da babban kuskure na siyasa da Trump ya tafka, ya kuma zubar da mutuncin Amurka a idon duniya.

Kungiyar tarayya Turai ta bakin babbar jami'arta mai kula da harkokin ketare, Frederica Mogherini, ta jaddada ci gaba da yin aiki da yarjejeniyar. 

Ita kuwa kasar Siriya tir ta yi da matakin tana mai danganta shi da rashin adalci, a yayin da kasar Turkiyya ta nuna shakku akan yanayin da za'a iya shiga a yankin dake fama da rikici.

Shi kuwa firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu yabawa ya yi da matakin na Trump tare da jinjina masa.

Ita dai kasar Saudiyya ta fitar da wata sanarwa a hukumance tana mai yin maraba da matakin na Trump kan janye jiki daga yarjejeniyar.

Dama dai Saudiyya da Isra'ila su ne suka yi ruwa da tsaki wajen hura wa Trump kunne kan ya janye daga yarjejeniyar wacce suka danganta da babbar barazana gere su kuma a cewarsu ba zata taba hana Iran mallakar makamin nukiliya ba.

Da take maida martanin jin kadan bayan sandar da janyewar Amurka daga yarjejeniyar, Jamhuriya Musulinci ta Iran ta bakin shugaban kasar Hassan Rohani, ta ce wannan ya nuna cewa ''Amurka kasa ce da ba zata taba cika alkawarinta ba''

A yanzu dai Iran ta ce tana nazarin fara tattaunawa da kasashen Turai, da China da kuma Rasha don ganin idan zasu iya ci gaba mutunta yarjejeniyar don ci gaba da aiki da ita, saidai bai yanke shawarar ko Iran din zata koma kan shirinta na tatse urenium.