Amurka : Kuskure Ne Ya Janyo Kashe Mana Sojoji A Nijar
https://parstoday.ir/ha/news/world-i30716-amurka_kuskure_ne_ya_janyo_kashe_mana_sojoji_a_nijar
Ma'aikatar tsaron Amurka ta Pantagon ta yarde cewa an kashe sojojinta hudu ne a kauyen Tongo Tongo dake nisan kilomita 100 daga Yamai babban Nijar a iyaka da Mali bisa rashin shiri da gazawa wajen sanya ido.
(last modified 2019-04-27T14:25:10+00:00 )
May 11, 2018 05:09 UTC
  • Amurka : Kuskure Ne Ya Janyo Kashe Mana Sojoji A Nijar

Ma'aikatar tsaron Amurka ta Pantagon ta yarde cewa an kashe sojojinta hudu ne a kauyen Tongo Tongo dake nisan kilomita 100 daga Yamai babban Nijar a iyaka da Mali bisa rashin shiri da gazawa wajen sanya ido.

Rahoton da Pantagon ta fitar ya ce 'yan ta'addan IS ne dauke da muggan makamai da gurneti da bindigogi masu aman wuta suka kashe sojojin na ta a kasar ta Nijar a watan Oktoba na 2017 data gabata.

Sakamakon binciken mai shafuka takwas da ma'aikatar ta Pantagon ta gudanar cikin sirri, ya nuna cewa akwai kura kurai da kuma gazawa wajen shiri wanda ya kai ga aukuwar mummunan al'amarin. 

Rahoton ya ce an yi shirin ne da nufin ''gano wa, sannan idan dama ta samu kuma a cafko wani jigon reshen kungiyar IS a yankin Sahara da Adnan Abu Walid Sahrawi ke jagoranta, amma sakamakon binciken na Pantagon ya nuna cewa kwamandan shirin sintirin bai fayyace ainahin aikin da za'a aiwatar ba ta yadda zai tafi daidai da yanayin da ake ciki a yankin, hasali ma, kamata ya yi a samu umurnin daga babban kwamandan tawagar sojojin dake da mazauni a kasar Chadi.

Su dai sojojin na Amurka sun je kasar ta Nijar ne don baiwa sojojin kasar horo da kuma taimaka masu wajen yaki da ta'addanci.