'Yan Wasan Kwallon Kafan Mata Na Iran Sun Zama Zakarun Asiya
(last modified Sun, 13 May 2018 05:33:10 GMT )
May 13, 2018 05:33 UTC
  • 'Yan Wasan Kwallon Kafan Mata Na Iran Sun Zama Zakarun Asiya

Kungiyar kwallon kafa ta mata na cikin na cikin dakin wasa da aka fi sani da Futsal na Iran ta zama zakaran zakarun nahiyar Asiya bayan da ta lallasa takwararta na kasar Japan da ci 5-2.

Kungiyar kwallon kafa ta matar ta Iran ta sami wannan nasarar ce a wasan karshe na gasar cin kofin zakaran zakarun nahiyar Asiyan da aka gudanar a birnin Bangkok, babban birnin kasar Thailand inda 'yan matan na Iran suka lallasa abokan karawarsu na kasar Japan din da ci  5-2.

Shugaban kasar Iran Dakta Hasan Rouhani da sauran jami'an kasar ta Iran sun taya 'yan kungiyar kwallon kafa ta matan murnar wannan nasara da suka samu na zama zakarun na Asiya wanda da man a hannunsu yake.

Kafin wasan na jiya dai, kungiyar kwallon kafa ta mata ta kasar Thailand mai masaukin baki ita ce ta zamanto ta uku bayan da ta sami nasara a kan kasar Vietnam da ci 3-2 a bugu daga kai sai mai tsaron gida da aka gudanar a tsakaninsu a wasan da suka yi don zaban na uku a gasar.