Biritaniya : An Dakile Hare-Haren Ta'addanci 12
(last modified Mon, 14 May 2018 19:02:13 GMT )
May 14, 2018 19:02 UTC
  • Biritaniya : An Dakile Hare-Haren Ta'addanci 12

Shugaban hukumar yansandan ciki na kasar Britani MI5 ya bada rahoton cewa hukumarsa ta sami nasarar haka shirye-shiryen ayyukan ta'addanci a wurare daban daban a duk fadin kasar har sau 12 tun watan Maris na shekara ta 2017 ya zuwa yanzu.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Andrew Parker shugaban hukumar MI-5 na kasar Britania yana fadar haka a yau litinin a wani taron harkokin tsaro da ake gudanarwa a halin yanzu a birnin Balin na kasar Jamus.

Parker ya yi gargadi ga kasashen turai kan cewa akwai yiyuwan kungiyar yan ta'adda ta Daesh bayan an sami nasara a kana a kashen Asia ta yi kokarin shigowa turai don aiwatar da ayyukan ta'addanci. 

Shugaban na MI-5 ya kara jaddada korewar ma'aikatansa wajen kare mutanen kasar Britania daga duk wata barazanar tsaro da zata kunno kai a kasar.

A halin yanzu dai kasar Britania tana kan marhala barazanar aukuwar ayyukan ta'addanci na 4 cikin marhaloli 5, wanda yake nuna cewa barazanar yiyuwan kai hare-haren ta'addancin yana da yawa a kasar.