Wata Tawagar Amurka Ta Isa Koriya Ta Arewa
Shugaba Donald Trump na Amurka ya tabbatar da cewa, wata tawagar jami'an kasar sun isa Koriya ta arewa don tattaunawa game da shirye-shiryen ganawarsa da shugaba Kim Jong Un da aka shirya gudanarwa a ranar 12 ga watan Yuni a Singapore.
Shugaba Trump ya sanar da hakan ne jiya Lahadi a shafinsa na Tweeter. Ya ce yana da imanin cewa, Koriya ta arewa tana da albarkatu, kuma wata rana za ta kasance babbar kasa a fannin tattalin arziki da harkokin kudi, kuma shugaba Kim Jong Un ya yarda da kalaman na Trump.
A jiya Lahadi ne dai jaridar Washington Post ta ba da labarin cewa, tsohon jakadan Amurka a Koriya ta Kudu Sung Kim ya tsallaka kasar Koriya ta arewa inda ya gana da mataimakin ministan harkokin wajen kasar Koriya ta Arewan Choe Son Hui game da shirye-shiryen taron kolin shugabannin kasashen biyu.