Rikicin Siyasar Kasar Nicaragua Ya Lashe Rayukan Mutane Kimanin 100
Zanga - zangar nuna kin jinin gwamnatin kasar Nicaragua ta lashe rayukan mutane akalla 98 tare da jikkata wasu adadi mai yawa.
Kamfanin dillancin labaran Faransa ya watsa rahoton cewa: Zanga-zangar da al'ummar Nicaragua suka fara tun a tsakiyar watan Aprilun wannan shekara ta 2018 zuwa yanzu, zanga-zangar ta janyo hasarar rayukan mutane akalla 98 tare da jikkatan wasu fiye da 79 na daban.
Zanga-zangar nuna kin jinin gwamnatin Nicaragua ta samo asali ce tun bayan wata sanarwa da shugaban kasar Daniel Ortega ya gabatar da a ciki ya bayyana shirin gwamnatinsa na gudanar da gyarar fuska a harkar kudin ritaya na ma'aikatan gwamnati wato fansho lamarin da zai janyo samun kudin ritaya kadan bayan shafe tsawon shekaru ana gudanar da aiki karkashin gwamnatin kasar ta Nicaragua.
Bayan bullar zanga-zangar kin amincewa da wannan sabon shiri na gwamnatin Ortega, shugaban kasar ya sanar da janye aniyarsa ta gudanar da gyarar fuskar amma al'ummar kasar suka ki janye aniyarsu ta nuna kin jinin gwamnatin Nicaragua lamarin da ya janyo ci gaba da tarzoma a sassa daban daban na kasar ciki har da birnin Managua fadar mulkin kasar.