Harajin Karafa : Kungiyar EU Ta Kai Karar Amurka
(last modified Fri, 01 Jun 2018 15:34:19 GMT )
Jun 01, 2018 15:34 UTC
  • Harajin Karafa : Kungiyar EU Ta Kai Karar Amurka

Kungiyar tarayya turai, ta EU, ta ce ta kai karar Amurka, gaban hukumar kasuwanci ta duniya, bayan da Amurkar ta sanar da fara aiki da sabon tsarin biyan harajin karafa.

Matakin na Amurka dai ya shafi karin biyan harajin karafa da 25% da kuma na 10% akan samfolo ga kasashen Turan da Canada da kuma Mexico.

Shugabar kwamitin kungiyar tarayya turai, Cecilia Malmström, ta bayyana a wani taron manema labarai birnin Brussuls cewa, kasashen turan na adawa da matakin na Amurka.

Yau 1 ga watan Yuni ne dai matakin na Amurka ya fara aiki, akan dukkan karafa da ake shigo dasu daga kasashen turai.

Kungiyar ta EU, ta kuma sanar da shigar da karar China, gaban hukumar ta WTO, akan karkata fasahohin kamfanonin kasashen Turai dake China ta bayan fage.