An Gudanar Da Ranar Qudus Ta Duniya A Kasar Amurka
Al'ummar Amurka sun gudanar da zanga-zangar ranar Qudus ta duniya a birnin NewYork na kasar suna Allah wadai da zaluncin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila kan al'ummar Palasdinu.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya watsa rahoton cewa: Wasu daruruwan al'ummar Amurka sun gudanar da zanga-zangar ranar Qudus ta Duniya a jiya Juma'a a birnin NewYork suna rera taken yin Allah wadai da zaluncin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila kan al'ummar Palasdinu tare da jaddada wajabcin kawo karshen mamaye yankunan Palasdinawa.
Har ila yau masu zanga-zangar sun daga kwalaye da tutuci masu dauke da rubutun cewa: Kasar Palasdinu mallakin Palasdinawa ce. Kamar yadda masu zanga-zangar suka jaddada yin kira ga shugaban Amurka Donald Trump da ya janye daga goyon bayan zaluncin Yahudawan Sahayoniyya domin bai wa Palasdinawa 'yan gudun hijira hakkin komawa kasarsu ta gado.