An Raya Ranar Qudus Ta Duniya A Birnin Hague
(last modified Sun, 10 Jun 2018 06:55:33 GMT )
Jun 10, 2018 06:55 UTC
  • An Raya Ranar Qudus Ta Duniya A Birnin Hague

Dariruwan mutane ne suka gudanar da jerin gwano na raya ranar Qudus ta Duniya a birnin Hague na kasar Holland

A jiya asabar, dariruwan 'yan kasar Holland dauke da tutar Palastinu ne suka gudanar da jerin gwano har zuwa gaban Majalisar dokokin kasar,  inda suke rera taken yin alawadai da ta'addancin haramtacciyar kasar Isra'ila da Amurka.

A cikin sanarwar da suka fitar mahalarta zanga-zangar  sun yi alawadai kan gisan gillar da ya sabawa adamtaka na yahudawan sahayuwa kan al'ummar Palastinu tare neman kawo karshen killacewar da ake yiwa yankin zirin Gaza.

A cikin wani bangare na bayyanin sun ce ranar Qudus dake a matsayin Sunnar margayi Imam Khomeini (Q.S), alami ne na hadin kan al'ummar musulmi wajen goyon bayan al'ummar  Palastinu da akwa sama da shekaru 60 ana zalinta.

Kimanin shekaru 39 kenan marigayi Imam Khumaini ya  sanya ranar juma'ar karshe ta watan Ramalana a matsayin Ranar Kudus ta duniya don nuna goyon baya ga al'ummar Palastinu yana mai kiran al'ummar musulmi da su girmama wannan ranar.