Kungiyar Tarayyar Turai Zata Kakabawa Sojojin Myanmar Takunkuman Tattalin Arziki.
(last modified Mon, 25 Jun 2018 18:58:39 GMT )
Jun 25, 2018 18:58 UTC
  • Kungiyar Tarayyar Turai Zata Kakabawa Sojojin Myanmar Takunkuman Tattalin Arziki.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran, ta bayyana cewa jami'an sojojin Myanmar 7 ne takunkuman na tarayyar Turai za su shafa, sanadiyyar rawan da suka taka wajen take hakkin bil'adama a kan yan kabilar Rokhinga a yankin Rokhin a shekara da ta gabata.

Majiyoyin diblomasiyyar tarayyar ta Turai ta kara da cewa takunkuman, wadanda zasu fara aikin a yau Litinin zasu hada da sandarar da dukiyoyinsu da ke kasashen Turai da kuma hanasu tafiye tafiye zuwa kasashen kungiyar. Kafin haka dai kungiyar ta EU ta tsawaita takunkuman makamai da ta dorawa gwamnatin kasar ta Myanmar.

Kafin haka ma gwamnatin Amurka ta dorawa kasar Ta Myanmar takunkumai a cikin watan Decemban shekarara da ta gabata, sannan kasar Canada ma ta dauki irin wannan matakin bayan kisan kiyashin da aka yiwa Musulmi a garin Inn Din na lardin Rokhin na kasar ta Myanmar a shekara da ta gabata.

A halin yanzu dai yan jarida 2, wadanda suka bada rahoton kissan na Inn Din, wadanda kuma suke aiki da kamfanin dillancin labaran Reuters suna tsare. Akwai yuwa a dauresu shekaru 14 a gidan kaso sanadiyyar bada rahoton asiran kasarsu.