An Zargi Amurka Da Taimaka Ma Kungiyar 'Yan Ta'adda Ta Daesh
(last modified Thu, 28 Jun 2018 22:00:43 GMT )
Jun 28, 2018 22:00 UTC
  • An Zargi Amurka Da Taimaka Ma Kungiyar 'Yan Ta'adda Ta Daesh

A cikin wani bayanin da ta fitar, cibiyar da ke sanya ido kan harkokin tsaro a nahiyar turai ta bayyana hare-haren da jiragen yakin Amurka suka kaddamar kan dakarun sa ka na kasar Iraki da cewa, hakan yana matsayin taimaka 'yan ta'addan Daesh ne.

Shafin Al-sharah ya habarta cewa, bayanin da ofishin babban sakataren kungiyar ya fitar ya nuna cewa, babu wani dalili da zai sanya Amurka da kaddamar da hari kan dakarun sa kai na kasar Iraki wato Hashdu Sha'abi, domin kuwa wadannan dakaru suna yaki da ta'addancin Daesh ne.

Bayanin ya ce kai wadannan hare-hare a kan dakarun Hashdu Sha'abi, yana matsayin taimaka ma Daesh ne, kamar yadda cibiyar ta ce baya ga haka ma akwai dalilai da dama da suke tabbatar da cewa Amurka tana bayar da muggan makamai ga 'yan ta'addan Daesh, gami da makudan kudade.

Amurka dai ta yi ta kokarin nisanta kanta daga harin, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mayakan sa kai na kasar Iraki fiye da 20, a lokacin da suke shirin kai farmaki kan wani gungun 'yan ta'addan Daesh a kan iyakokin Iraki da Syria.