Faransa Ta Bukaci Karin Hadin Kan Kungiyar Turai Domin Kalubalantar Amurka
Ministan Kudin kasar Faransa ya ce wajibi ne Kasashen tarayyar Turai su kara hada kansu wajen kalubalantar barazanar shugaban kasar Amurka
Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya nakalto ministan kudin Faransa na neman kasashen Turai da suka hada kansu wajen kalubalantar barazanar shugabar Amurka domin kare tattalin arzikin kasashensu, kuma bai dace kungiyar EU ta shiga tattauna da Amurka ba matukar ba ta janye matakin da ta dauka na karin haraji ga kayen Turan dake shiga kasar Amurka ba.
Wannan martani na zuwa ne a yayin da Shugabar gwamnatin Jamus Angela Markel ke cewa tana goyon bayan Amurka kan matakin da kungiyar EU ta dauka na rage harajin Motocin Amurka.
Wata majiya a ma'akatar kudin Faransa na cewa wajibi ne kasashen Turai su dauki matsaya guda a game da kasar Amukra.
Kafin haka dai gwamnatin Amurka ta dorawa bakin farfe da kuma karfen alluminium da suke fitowa daga kasashen turai haraji , sannan a cikin watan Maris da ya gabata gwamnatin shugaban trump ta takaita yawan karafan da zasu shigo kasar daga tarayyar Turai.
A wani bangare kuma kasashen Mexico, Canada da kuma China duk sun dauki matakan maida martani ga harajin na gwamnatin shugaba Trump.