Koriya Ta Arewa Ta Kalubalaci Tattaunawarta Da Amurka
(last modified Sat, 07 Jul 2018 16:25:11 GMT )
Jul 07, 2018 16:25 UTC
  • Koriya Ta Arewa Ta Kalubalaci Tattaunawarta Da Amurka

Koriya ta Arewa ta kalubalanci yadda tattaunawarta da Amurka ke tafiya, kwanaki biyu bayan ganawar da bangarorin biyu ke yi kan yarjejeniyar nukiliya.

Kafn hakan dai sakataren harkokin wajen Amurkar, Mike Pompeo, ya fada wa manema labarai a lokacin da ya isa birninTokyo cewa, ana samun ci gaba sosai a tattaunawar.

Bayan dai Ponpeo ya bar binrnin Pyanyang, ministan harkokin Koriya ta Arewar ya ce tattaunawar bata tafiya kamar yadda aka tsara a yarjejeniyar da shugabannin kasashen biyu suka cimma a ranar 12 ga watan Yuli da ya gabata a Singapore.

Mahukuntan Pyangyand sun ce bukatun da Amurka ta gabatar a tattaunawar akwai son kai ciki sosai, musamman kan batun shirin lalata makamam nukiliya Koriya ta Arewar. , kamar yadda kamfanin dilnacin labaren Koriya ta kudu ya rawaito.