Za A Yi Sabbin Dokoki Akan Musulmin Faransa
Jul 10, 2018 12:30 UTC
Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ne ya bayyana haka a gaban majalisar dokokin kasar inda ya ce; A cikin wannan shekarar ta 2018 za yi dokoki da sabbin tsare-tsare ga musulmin kasar.
Macron ya kara da cewa; Musulunci shi ne addini na biyu a cikin kasar Faransa domin haka yana da bukatuwa da a yi sabbin tsare-tsare da dokoki a kansa. Bugu da kari Macron ya ce; Gwamnatin Faransa ba ta da wata matsala da addinin musulunci ko kadan.
Shugaban na Faransa ya bayyana haka ne alhali a cikin shekarun bayan an an yi dokokin da suke takurawa musulmi, kamar hana yin salla a cibiyoyin hukuma haka nan hana mata sanya suturar hijiba.
Tags