Kasar Canada Ta Soki Matsayar Trump Akan Kungiyar Tsaro Ta "Nato"
Justin Trudeau mai da martani akan kiran da Trump ya yi wa kasashen mambobi na Nato da su rika biyan kungiyar kaso biyu cikin dari da kudaden shigarsu, yana cewa; wane alfanu ne hakan zai haifar?
Fira minitsan kasar ta Canada ya yi kira da a sami hadin kai a tsakanin kasashen kungiyar domin fuskantar kalubalen da yake gabansu.
A jiya laraba ne shugaban na kasar Amurka ya zargi wasu kasashen mambobi a yarjejeniyar tsaro ta Nato da rage kudaden da suke bayarwa ga kungiyar yana mai cewa: Wajibi ne su kara kasafin kudinsu na soja daga kaso biyu na kudaden shigarsu zuwa kaso hdu cikin dari.
Tun da fari, shugaban na kasar Amurka ya ce; kamata ya yi ace kudaden da sauran kasashe za su bayar ya zama mai yawa, na Amurka kuma ya zama kadan.
A yau alhamis ne dai ake kawo karshen taron na Nato.