Ganawar Trump Da Putin Ta Bar Baya Da Kura A Amurka
Ganawar da Shugaba Donald Trump na Amurka ya yi da takwaransa na Rasha, Vladimir Putin, ta haddasa kace nace ba kadan ba a Amurka, inda 'yan jam'iiyar Demokrate har ma da bangaren 'yan Repablicain ke cewa Trump ya kasa abun fadi gaban Putin.
Shugaban 'yan Demokrate Sanata, Chuck Schumer, ya zargi Trump da kasawa da kuma rashin abin fadi a gaban takwaran nasa na Rasha.
Babbar ayar tambaya da ake jiran amsarta daga fadar White house ita ce '' ko mi ya sa Trump ya fifita manufofin Rasha sama da na Amurka'', a cewar Sanata Schumer a shafinsa na Twitter.
Shi kuwa Sanata John McCain, na 'yan Repablicain danganta lamarin ya yi da abu mafi muni da Shugabancin Amurka ya gani a tsawan tarihi, a yayin da wasu sanatocin ke cewa Rasha ba abokiyar tafiyarsu ce ba.
A yayin ganawar shuwagabannin biyu, ta jiya Litini a Helsinki, Trump dai ya ki yin allawadai da zargin da ake wa Rasha na kutse a harkokin zaben Shugaban Amurka, wanda shi ne babban abunda Amurka suka zura ido akai.
A nasa bangare dai shugaban kasar ta Rasha, Vladimir Putin, sake yin fatali ya yi da zargin, yana mai cewa bai ga dalilin dai zai sa kasarsa ta yi hakan ba.