Macron Ya Soki Ayyukan Tarayyar Turai
Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya soki tarayyar turai saboda rashin gudanar da ayyuka yadda ya kamata
Shugaban na kasar Faransa wanda ya gabatar da taron manema labaru na hadin gwiwa da takwaransa na kasar Sabia, Alexander Va ya ce; Saboda sabanin da ake da shi a tsakanin kasashe mamabobi 28 na tarayyar turai din, ayyuka ba su tafiya kamar yadda ya kamata
Bugu da kari shugaban na kasar Faransa ya yi kira da samar da yanayin da zai bai wa kasar ta Sabia damar zama memba a tarayyar turai.
Sai dai shugaban na kasar Faransa ya ce gabanin tarayyar turai din ta fadada ya kamata a yi mata gyare-gyare.
A nashi gefen shugaban kasar Sabia ya ce kasarsa a shirye take ta yi aiki da tsari da kuma sharuddan tarayyar ta turai.