Ci Gaba Da Cacar Baki Tsakanin 'Yan Siyasar Amurka
(last modified Wed, 18 Jul 2018 18:15:06 GMT )
Jul 18, 2018 18:15 UTC
  • Ci Gaba Da Cacar Baki Tsakanin 'Yan Siyasar Amurka

Shugaban kasar Amurka ya ce masu sukansa a tsakanin 'Yan siyasar kasar sun hadu da tabin hankali

A cikin wani sako da ya rubuta a shafinsa ta Twitwer Shugaban kasar Amurk Donal Trump ya mayar da martani kan masu sukansa kan ganawarsa da takwaransa na kasar Rasha Viladimin Putin, inda ya ce masu kusansa daga cikin 'yan siyasa na bangaren jam'iyar  Republicain ko Demokrat, sun  kamu da cutar tabin hankali.

Trump ya kara da cewa da dama daga manyan jami'an leken asirin Amurka sun nuna amincewarsu da abinda ya fada a taron manema labarai na kasar Finland.

A ranar Litinin da ta gabata ce shugabanin biyu suka gana a birnin Helsinki na kasar Finlan, inda a yayin da suke gudanar da taron manema labarai, Shugaba Trump ya ce babu wani dalili dake tabbatar da cewa Rasha ta yi kutse a zaben Amurka na 2016.

Wannan kalamai dai na Shugaba Trump  ya fuskanci suka da kakkausan lafazi daga manyan 'yan siyasar kasar hatta na jam'iyar Republicain inda alal misali John McCain daya daga cikin shika-shiken jam'iyyar ya bayyana kalaman da shugaba Trump ya yi a gaban Shugaba Putin a lokacin ganawar tasu, da kasancewa abin kasakanci mafi girma da wani shugaban Amirka ya taba yi a gaban shugaban wata kasa a tsawon tarihi.