Trump Ya Ce A Shirye Yake Ya Tattauna Da Iran
(last modified Tue, 31 Jul 2018 07:25:22 GMT )
Jul 31, 2018 07:25 UTC
  • Trump Ya Ce A Shirye Yake Ya Tattauna Da Iran

A yayin da yake ci gaba da tsanata yin barazana da kuma bayyana kiyayarsa ga al'ummar kasar Iran, Shugaban Amurka Donal Trump ya ce a shirye yake da tattauna da hukumomin jamhoriyar musulinci ta Iran,duk lokacin da suke so, ba tare da gindaya sharadodi ba.

Trump wanda ya bayyana haka yayin ganawa da manema labarai tare da Firaministan Italia Guiseppe Conte  a marecen jiya Litinin ya ce zai gana da shugabannin Iran muddin suna bukatar haka.

Wannan sauyin matsayi na zuwa ne kasa da mako guda bayan shugaba Trump ya gargadi shugaban Iran Hassan Rouhani cewar muddin suka cigaba da yiwa Amurka barazana za su gamu da fushin da ba su taba gani ba a tarihin duniya.

Tun kafin rantsar da Donald Trump a matsayin shugaban Amurka ya soki yarjejeniyar nukiliyar da Amurka tare da kasashen duniya suka kulla da Iran, yayin da ya yi watsi da shirin bayan ya hau karagar mulki.

A makon jiya, jami’an kasar Iran sun bayyana cewar sau 8 shugaba Trump ke bukatar ganawa da shugaba Hassan Rouhani lokacin gudanar da taron Majalisar Dinkin Duniya amma shugaban na Iran na hawa kujerar naki.

Hukumomin Jamhoriyar musulinci ta Iran sun bayyana cewa tattauna da Amurka ba shi da wani amfani, ganin cewa hukumomin kasar ba su da alkawari.