Trump Na Tsammanin Tattaunawa Da Iran Nan Ba Da Jimawa Ba
Shugaba Donald Trump, na Amurka ya sake dauko batun tattaunawa da Iran, inda a cewarsa hakan zata wakana nan bada jimawa ba.
Wannan dai na zuwa ne bayan da Trump din ya bayyana a ranar Litini cewa a shirye yake ya tattauna da hukumomin na Iran, duk lokacin da suke so, ba tare da gindaya sharuda ba.
Manyan jami'an Jamhuriya Musulinci ta Iran dai har yanzu basu ce uffan ba kan tayin na Trump, amma wasu daga cikin 'yan siyasar kasar ta Iran sun danganta bude tattaunawa da Trump da abun kunya.
Wani mashawarcin shugaban Iran, mai suna Hamid Abutalebi, ya bayyana cewa tattaunawa da Amurka zata soma ne da mutunta al'ummar ta Iran da rage nuna kiyaya gare su da kuma dawowar Amurka a cikin yarjejeniyar nukiliyar Iran.