Kyamar Salon Mulkin Donald Trump Na Karuwa A Kasar Amurka
Wani sakamakon jin ra'ayin jama'a da aka gudanar a kasar Amurka ya nuna cewa, mafi yawan Amurkawa ba su gamsu da salon mulkin Donald Trump ba.
Tashar talabijin ta CNN ta bayar da rahoton cewa, cibiyar Monmouth ta gudanar da wani jin ra'ayin jama'a a tsakanin Amurkawa a dukkanin fadin kasar, dangane da gamsuwa ko rashin gamsuwarsu da salon mulkin Donald Trump, inda sakamakon ya nuna cewa kimanin kashi 57 na Amurkawa ba su gamsu salon siyasar Trump ba.
Wasu daga cikin masana kan harkokin siyasar kasar ta Amurka da tashar CNN ta zanta da su, sun bayyana cewa wannan sakamakon ya nuna cewa adadin masu adawa da salon mulkin Trump a tsakanin Amurkawa yana karuwa.
Haka nan kuma sun bayyana cewa zai yi tasiri ga zaben 'yan majalisar dokokin kasar da za agudanar a cikin watan Nuwamba mai zuwa.