Shugaban Kasar Amurka Na Iya Fuskantar Kiran Majalisar Dokokin Kasar
(last modified Wed, 22 Aug 2018 18:59:13 GMT )
Aug 22, 2018 18:59 UTC
  • Shugaban Kasar Amurka Na Iya Fuskantar Kiran Majalisar Dokokin Kasar

Mujallar Newsweek da ta fito a yau Laraba ta ce sauyin da ake samu a kan batun Paul Manafort, ya sa Shugaba Donlad Trump na karatar gurfana a gaban majalisa domin amsa tambayoyi

Paul Manfort wanda tsohon yakin neman zaben Trump ne da kuma Micheal Cohen tsohon lauyan shugaban kasar. Kafafen watsa labarun Amurka suna bayyana cewa fitowar sabbin bayanai akan mutane biyu da aka samu a jiya Talata, yana a matsayin mai ban mamaki.

A jiya Talata ne Manafort ya gurfana a gaban kotu a jahar Virginia, kuma an tabbatar da laifin almundahanar kudaden Banki da na haraji  a kansa.

Shi ma Cohen ya yi furuci da aikata laifi a gaban wata kotu a birnin Newyork.

Ana sa Ido domin ganin ko za a dangata laifukan da mutanen biyu su ka aikata suna da alaka ta kai tsaye da shugaban kasar Donald Trump, wanda hakan zai iya kai wa ga kiran shi domin ya yi bayani