MDD ta dauki kudirin tura Dakarun sulhu zuwa kasar Burundi
(last modified Sun, 03 Apr 2016 04:10:26 GMT )
Apr 03, 2016 04:10 UTC
  • MDD ta dauki kudirin tura Dakarun sulhu zuwa kasar Burundi

Yan Adawa A kasar Burundi Sun bayyana rashin jin dadinsu kan matakin da MDD ta dauka na aikewa da jami'an 'yan sanda zuwa kasar

Kamfanin dillancin labaran Reuteus ya nakalto Leon Ngadakomanak shugaban jam'iyar tabbatar da democradiya na kasar Burundi ya ce bukatar jam'iyun Adawa shine a turo Dakarun tsaro da sulhu na Majalisar dinkin Duniya wadanda za su tilastawa kungiyoyin dake dauke da makamai musaman kungiyar da gwamnati ta kafa ajiye makamansu.

Wannan mataki da MDD ta dauka a jiya Assabar shine abinda Gwamnatin ta Burundi ta bukata.

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da wani kudiri da zai bada damar turawa da jami'an 'yan sanda Burundi, don kiyaye zaman lafiya da ke tangal-tangal a wannan kasa. Babban Sakataren majalisar Ban Ki-Moon ne aka kayyade ma wa'adin kwanaki 15 don nazarin kan yadda zai aiwatar da wannan kudiri.

Idan dai za a iya tunawa kasar Burundi ta fada cikin rikicin siyasa tun bayan da shugaba Pierre Nkurunziza ya dage kai da kafa a kan sai ya yi tazarce, duk da cewar kundin tsarin mulkin kasar ya haramta masa tsayawa takara. Fiye da mutane 400 ne suka rasa rayukansu a wannan rikici, yayin da wasu dubbai kuma suka kaurace wa mahalansu.

Jakadan Faransa a Majalisar Dinkin Duniya Francois Delattre ya ce kasarsa ta shigar da wannan daftari ne saboda ta damu da ganin cewar an samu zaman lafiya a Burundi.