Gangamin Nuna Kin Amincewa Da Yunkurin Hana Saka Lullubi A Austria
(last modified Fri, 14 Sep 2018 17:38:01 GMT )
Sep 14, 2018 17:38 UTC
  • Gangamin Nuna Kin Amincewa Da Yunkurin Hana Saka Lullubi A Austria

Kungiyoyin kare hakkokin bil adama da dam ne suka shirya gangamin kin amincewa da daftarin dokar hana dalibai musulmi mata saka hijabi.

Kamfanin dillancin labaran Anatoli ya bayar da rahoton cewa, a jiya daruruwan mambobin kungiyoyin kare hakkokin bil adama da na farar hula ne suka shirya gangamin kin amincewa da daftarin dokar hana dalibai musulmi mata saka lullubi a makarantu.

Wannan matakin dai ya biyo bayan da ministan ilimi na kasar Austria ya bukaci 'yan majlaisar dkokin kasar ne da su fitar da wata doka wadda za ta hana dalibai mata musulmi da kuma malmai mata musulmi saka lullubi a makarantun sakandare na kasar.

Majalisar dokokin kasar Austria ta rubuta wannan a matsayin wani daftarin kudiri da za ta tattauna domin duba yiwuwar hakan ko kuma rashinsa.

Tuna  cikin shekara ta 1912 aka amince da addinin musulunci a matsayin da daya daga cikin addinin kasar Austria  a hukumance, inda yanzu adadin musulmin kasar ya haura dubu 600 da 'yan kaia.