Shirin Ficewar Birtaniya Daga Turai Yana Neman Gaggara
(last modified Sat, 22 Sep 2018 06:25:05 GMT )
Sep 22, 2018 06:25 UTC
  • Shirin Ficewar Birtaniya Daga Turai Yana Neman Gaggara

Fira ministar Birtaniya Theresa May ce ta bayyana cewa tattaunawar da ake yi domin ficewar kasar daga trayyar turai ya ci tura

Theresa May wacce ta fitar da wani bayani a jiya juma'a ta ce; London ba za ta karbi shawarwarin da tarayyar turai ta gabatar ba na yadda ya kamata ta fice daga cikin tarayyar.

Fira ministar ta Birtaniya ta mayar da martani ne akan sakamakon taron da shugabannin tarayyar turai su ka yi a ranakun Laraba da Alhamis a kasar Austria, inda su ka tattauna hanyoyin da ya kamata Birtaniyan ta fice daga tarayyar.

Muhimman batutuwan da su ka kawo cikas a tattaunawar sun kunshi na iyakokin da aka yi tarayyar a tsakanin Jamhuriyar Ireland da Birntaniyan da kuma kula da kai da komowar haja.

Tattaunawar da ake yi tana nufin fitar da Ireland ta Arewa daga hadaddiyar kasuwar turai, sannan kuma da samar da iyaka a tsakanin Ireland ta arewa da ta kudu.

Theresa May ta bayyana cewa ba za ta lamunta da duk wani yunkuri da zai raba Birtaniya ba.