Shugaban Hukumar Interpol Ya Yi Murabus
https://parstoday.ir/ha/news/world-i33526-shugaban_hukumar_interpol_ya_yi_murabus
Hukumar ‘yan sanda ta kasa da kasa Interpol, ta sanar da cewa shugabanta Meng Hongwei ya yi murabus.
(last modified 2018-10-08T11:17:20+00:00 )
Oct 08, 2018 11:17 UTC
  • Shugaban Hukumar Interpol Ya Yi Murabus

Hukumar ‘yan sanda ta kasa da kasa Interpol, ta sanar da cewa shugabanta Meng Hongwei ya yi murabus.

Sanarwar da hukumar ta fitar, ta ce a halin yanzu, mataimakin tsohon shugaban Kim Jong yang na kasar Korea ta Kudu ne zai cigaba da rikon kwaryar shugabancin hukumar.

Nan gaba dai ne za'a zabi sabon shugaban da zai karasa wa'adin tsawon shekaru 2 na tsohon shugaban hukumar. 

Wanann dai na zuwa ne bayan da gwamnatin China ta tabbatar da kame shugaban hukumar mai murabus, domin gudanar da bincike akan zarge-zargen da ake masa na aikata laifin cin hanci da Rashawa a lokacin yana rike da mukamin karamin ministan al'umma na kasar a 2016.