Shugaba Trump Ya Amince Da Murabus Din Nicky Haley
(last modified Tue, 09 Oct 2018 19:14:43 GMT )
Oct 09, 2018 19:14 UTC
  • Shugaba Trump Ya Amince Da Murabus Din Nicky Haley

Shugaban kasar Amurka Donal trump ya amince da murabus din wakiliyar kasar a MDD Nicky Haley.

A cikin wata sanarwa da fadar White House ta fitar a wannan talata,Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya amince da murabus din Nicky Haley wakiliyar kasar ta Amurka a Majalisar Dinkin Duniya.

Sanarwar ta ce a makon da ya gabata, Nicky Haley ta tattauna da Shugaba Trump kan matakin da ta dauka na yin murabus.

Bayan rantsuwar kama aiki da shugaban Trump ya yi a shekarar 2017, ya zabi Nicky Haley ta kasance wakiliyar kasar a zauren Majalisar Dinkin Duniya, inda aka gabatar da ita a gaban sanatocin kasar, suka kuma amince da ita kan wannan mikami.

Har yanzu dai ba a bayyana dalilin da ya sanya Nicky Haley ta yi murabus daga kan mikaminta duk kuwa da cewa wannan murabus ya zowa da manyan jami'an gwamnatin Amurka da ba zata.

Rahotanin sun ce ba a taba samun wata Gwamnati a Amurka da ba ta cika shekaru biyu ba kamar wannan gwamnati wajen yawan yin murabus manyan jami'anta ko kuma korarsu daga bakin aiki.