Kashoggi : Duniya Na Ci Gaba Da Kauracewa Taron Saudiyya
A daidai lokacinda bayyanai ke ci gaba da fitowa kan bacewar dan jaridan nan na Saudiyya Jamal Kashoggi wanda ake zargi an yi masa kisan gilla ne a karamin ofishin jakadancin Saudiyya na Santanbul, su kuwa manyan kasashen duniya na ci gaba da sanar da kauracewa babban taron tattalin arzikin Riyad da za'a gudanar a wannan wata.
Sanarwar baya bayan nan ta fito ne daga sakataren harkokin kudin Amurka, Steven Mnuchin, wanda ya sanar da soke halartarsa a taron na Riyad.
Mista Steven, ya ce bayan tattauna da shugaba Trump da kuma sakataren harkokin wajen Amurkar, sun yanke shawarar ya kauracewa taron da za'a fara a ranar 23 zuwa 25 na watan nan a Riyad.
A wani labari kuma shugaba Trump ya ce Amurka ta karawa Saudiyya lokaci akan yi mata bayyani kan batun bacewar dan jaridan.
Tun kafin hakan dama ministan tattalin arzikin Faransa Brino Le Maire shi ma ya sanar da kauracewa taron har sai an ga abunda hali ya yi kan batun dan jaridan Kashoggi.
Shugaba Emanuelle Macron na Faransar shi ma ya ce kasarsa ta soke duk ziyara a hukumance zuwa Saudiyya har sai an san abunda ake ciki.
Dama dai shugabar bankin bada lamuni na duniya IMF, Cristine Lagarde ita ma ta soke halartar taronna Saudiyya.