MDD Za Ta Karfafa Dakarunta A Kasar Afirka Ta Tsakiya
(last modified Tue, 23 Oct 2018 11:47:58 GMT )
Oct 23, 2018 11:47 UTC
  • MDD Za Ta Karfafa Dakarunta A Kasar Afirka Ta Tsakiya

Saktare Janar na MDD ya bukaci a karfafa dakarun wanzar da zaman lafiya na MDD a kasar Afirka ta tsakiya.

Cikin wani jawabi da ya gabatar a gaban Kwamitin tsaro na MDD, Saktare janar na MDD Antonio Guterres ya yi ishara kan manyan zabuka biyu da a za a gudanar a shekarun 2020 da kuma 2021 a kasar Afirka ta tsakiya, inda ya bukaci rundunar wanzar da zaman lafiya ta MDD MINUSCA da ta kara azama wajen tabbatar da tsaro a kasar ta Afirka ta tsakiya musaman ma idan aka yi la'akari da yanayi tsoro da fargaba da wasu yankunan kasar ke ciki.

A tsakiyar watan Nuwambar wannan shekara ne aiki na MINUSCA zai kawo kawo karshe, to saidai mista Guterres ya bukaci karin wa'adi na ayyukan nasu har zuwa lokacin da tsaro zai tabbata a kasar. 

A halin da ake ciki dai akwai Sojoji dubu 11 da 650 dake aiki karkashin rundinar ta MINUSCA baya ga sojojin Faransa dubu biyu, dukkaninsu kuma suna aikin wanzar da zaman lafiya ne a kasar Afirka ta tsakiyan.