Rasha : Putin Zai Gana Da Trump A Binin Paris
Shugaba Vladimir Putin na kasar Rasha zai gana da takwaransa na Amurka Donald Trump a birnin Paris na kasar Faransa a watan Nuwamba mai zuwa.
Kamfanin dillancin labarai na kasar ta Rasha, ya ruwaito Mai taimakawa shugaban kasar Rasha Yury Ushakov na cewa, shugaba Putin ya gana da mai taimakawa shugaba Trump kan harkokin tsaron kasa John Bolton, wanda ke ziyara a kasar, inda suka tabbatar da cewa, shugabannin kasashen biyu wato Vladimir Putin da Donald Trump, za su gana da juna yayin da suke halartar bikin tunawa da cika shekaru 100 da kammala yakin duniya na farkon da za a shirya a birnin Paris a wata mai zuwa.
Ushakov ya bayyana cewa, ganawar da shugabannin biyu za su yi tsakaninsu irin ta yau da kullum ce, duk da cewa a halin da ake ciki yanzu, huldar dake tsakanin kasashen biyu ba ta gudana yadda ya kamata, amma ziyarar da Bolton ke yi a Rasha ta nuna cewa, gwamnatin Amurka tana son yin shawarwarin siyasa da gwamnatin Rasha, haka kuma bangaren Rasha shi ma yana wannan manufa.