Zaizayar Kasa Ta Ci Rayukan Mutane 21 A Kasar China
(last modified Mon, 29 Oct 2018 18:03:07 GMT )
Oct 29, 2018 18:03 UTC
  • Zaizayar Kasa Ta Ci Rayukan Mutane 21 A Kasar China

Kimanin ma'aikatan hako da ma'adinai 21 ne suka rasa rayukansu sanadiyar zaizayar kasa a gabashin kasar China.

Kafafin yada labaran gwamnatin kasar China sun habarta cewa zaizayar kasa ta rusa da wasu ma'aikatan hako da ma'adina 22 da suke cikin aiki  a jahar Shandong dake gabashin kasar .

Rahoton ya ce wannan zaizayar kasa ta yi sanadiyar hallakar ma'aikatan hako da ma'adinan 21, daya kadai ne daga cikin ma'aikatan ya samu nasarar tsira da ransa.

Tuni dai gwamnatin kasar ta China ta sanar da cewa a fara gudanar da bincike domin gano musababbin wannan girgiza kasa.

Shugaban kasar China ya meka ta'aziyarsa ga iyalan wadanda wannan hatsari ya ritsa da su.