Zaben Amurka: Jam'iyyar Republican Ta Sha Kaye A Zaben Majalisar Amurka
(last modified Wed, 07 Nov 2018 11:15:00 GMT )
Nov 07, 2018 11:15 UTC
  • Zaben Amurka: Jam'iyyar Republican Ta Sha Kaye A Zaben Majalisar Amurka

Jam'iyyar Democrats ta Amurka ta yi nasara a zaben rabin wa'adin zango bayan da ta doke jam'iyyar Republican a majalisar wakilan kasar, lamarin da ake ganinsa a matsayin gagarumin koma baya ga shugaban kasar Donald Trump.

Rahotanni daga Amurkan sun bayyana cewar sakamakon zaben yana nuni da cewa jam'iyyar Democrats din ta 'yan adawa ta sami kujeru 218 a majalisar a yayin da ita kuma jam'iyyar Repulican ta samu kujeru 193.

Sai dai a bangaren majalisar dattawan kasar kan jam'iyyar Republicans da ke da rinjaye a majalisar dattawa na kan hanyarta ta ci gaba da rike rinjayen da take da shi a majalisar da kujeru  51 yayin da Democrats ke da 49 a zauren majalisar.

Duk da cewa 'yan Republican din suna da rinjaye a majalisar dattawan wanda hakan zai iya ba wa shugaba Trump din damar zartar da kudurce-kudurcensa, to amma duk da hakan rasa majalisar wakilan da jam'iyyar Republican din ta yi da kuma yadda wasu 'yan jam'iyyar Republican din suke nuna adawa da wasu siyasarsa, hakan zai ci gaba da zama masa wani karfen kafa wajen aiwatar da abin da yake so.