'Yan Takara Mata Musulmi Sun Ci Zaben Majalisar Wakilan Amurka
Mata biyu da suka tsaya takarar neman kujerun majalisar wakilaia Amurka sun samu nasarar lashe zaben a jahohinsu.
Kamfanin dillancin labaran Anatoli ya bayar da rahoton cewa, majalisar shawara ta musulmin kasar Amurka ta nuna farin cikinta matuka dangane da nasarar da wadannan 'yan takara musulmi guda biyu suka samu.
'Yan takarar biyu su ne Rashida Tulaib da kuma Ilhan Umar, dukkansu sun tsaya ne a karkashin inuwar jam'iyyar Democrat, inda suka kayar da 'yan takarar jam'iyyar Republican mai mulki a kasar ta Amurka.
Ihan Umar dai 'yar asalin kasar Somalia ce da iyayenta suka yi gudun hijira zuwa Amurka tun tana da shekaru 12 da haihuwa, kuma ta tsaya takara ne a jahar Minnesota.
Ita kuma Rashida Tulaib 'yar asalin Palastine ce, kuma ta tsaya takara ne a jahar Michigan, inda za su kasance mata musulmi na farko da za su shiga majalisar dokokin kasar Amurka.
Jam'iyyar Democrat dai a wannan zaben ta kwace rinjaye a majalisar wakilan kasar ta Amurka, inda jam'iyyar Republican ta Donald Trump ta sha kayi.