An Soki Shugaba Trump Kan Korar Ministan Shari'ar Amurka
(last modified Thu, 08 Nov 2018 11:47:49 GMT )
Nov 08, 2018 11:47 UTC
  • An Soki Shugaba Trump Kan Korar Ministan Shari'ar Amurka

Wani Sanatan Amurka ya soki matakin da shugaban Trump ya dauka na tilastawa ministan shari'ar kasar yin murabus.

A wani sako da ya rubuta  kan batun yin murabus din ministan shara'ar kasar a shafinsa na  Twitter, Mista Bernie Sanders sanatan jahar Vermont ya ce bukatar yin murabus din na tsohon ministan shari'ar Jeff Sessions na zuwa ne bayan da ya fadawa shugaba Trump cewa wajibi ne a bawa Robert Mueller  mai bincike na musaman kan zargin Rasha da yin katsalandan a zaben Amurka na 2016 ya ci gaba da binciken da yake yi.

Wannan mataki da Trump ya dauka ya nuna cewa ba a shirye yake a gudanar da bincike kan lamarin ba, wanda kuma hakan ba a bu ne da za a lamince da shi a kasar ba.

Shugaban Amurka Donald Trump ya kori Ministan Shari’arsa Jeff Sessions, kwana guda da gudanar da zaben tsakiyar wa’adi, in da jam’iyyar Republican mai mulki ta rasa rinjaye a zauren Majalisar Wakilai.