Taron Zaman Lafiya A Birnin Paris
Nov 11, 2018 05:40 UTC
A wani lokaci yau Lahadi ne za'a bude wani taron kasa da kasa kan zaman lafiya a birnin Paris na kasar Faransa.
Taron na kwanaki uku na daga cikin bikin da ake na zagayowar cika shekara 100 da kawo karshen yakin duniya na farko.
Shuwagannin kasashen duniya dana gwamnatoci sama da 80 ne ake sa ran zasu halarci taron daga ranar 11 zuwa 13 ga watan Nuwamba nan a birnin na Paris.
Taron wanda na hadin gwiwa ne tsakanin shugaban Emmanuel Macron na Faransa da kungiyoyi masu zaman kansu, na da nufin neman hadin gwiwar kasashen duniya wajen wanzar da zaman lafiya mai dorewa tare da kawo karshen kalubalen da duniya ke fuskanta.
Tags