Khashoggi : Faransa Ta Sanya Takunkumi Ga 'Yan Saudiyya 18
Ma'aikatar harkokin wajen Faransa ta sanar da sanya takunkumin shiga kasar ga wasu 'yan Saudiyya 18 da ake zargi da hannu a kisan dan jaridan nan Jamal Khashoggi a karamon ofishin jakadancin Saudiyya na Santambul a ranar 2 ga watan Oktoba da ya gabata.
Sanarwar da ma'aikatar harkokin wajen Faransa ta fitar ta ce wannan matakin farko ne, don kuwa za'a iya tsawaita shi ko kuma a rage shi, gwargwadon yadda dai binciken da ake kan kisan dan jaridan zai bayar.
A ranar Litini data gabata ma dai kasar Jamus ta sanar da sanya takunkumi ga 'yan Saudiyyar 18, saidai sabanin Faransa, ksar ta Jamus ta sanya harda takunkumin sanyar da makamai ga Saudiyya.
Dama kafin hakan Amurka ta sanar da sanya wasu jerin takunkumi ga 'yan Saudiyya 17 da ake zargi da kisan dan Jaridan, saidai tuni masana suka fara danganta wadannan matakan dana jeka nayi ka ne kawai, don kuwa duk wadanda ake sanya wa takunkumi mutanen da Saudiyyar ta ce tana tsare da ne a gidajen kurkuku, sannan galibi ba'a bayyana sunayensu ba.