Mujallar Charlie Hebdo Ta Yi Dirar Mikiya Kan Musulmin Turai
Mujallar barkwanci ta kasar Faransa Charlie Hebdo ta yi dirar mikiya kan musulmin nahiyar turai, makonni biyu bayan kai harin ta'addanci a birnin Brussels na kasar Belgium.
A bugunta na jiya Litinin, mujallar ta buga makalar daya daga cikin shahararrun marubutanta Tijoo Col, wanda a cikin makalar tasa yake cewa, abin da ya faru a birnin Brussels da kuma wanda ya faru Paris a lokutan baya, ya tabbatar da cewa duk wani musulmi ba shi da wata makoma a nahiyar turai, inda ya ce babu wani banbanci tsakanin msuulmi mai tsatsauran ra'ay da mai sassaucin ra'ayi, dukkaninsu 'yan ta'adda ne, tare da yin kira da hana saka hijabi a dukkanin kasashen nahiyar turai.
Wannan makala dai ta fuskanci kakkausan martani daga bangarori daban-daban a kasar ta Faransa, daga masu mayar da martanin kuwa har da wadanda ba musulmi ba, inda suke bayyana wadannan kalamai da cewa na bangaranci ne da cin zarafi ga mabiya addinin muslunci, wadanda su ne farko wadanda suka yi Allawadai da hare-haren ta'addancin Paris da Brussels, tare da nisanta kansu daga ayyukan 'yan ta'adda masu da'awar jihadi.