Rasha Ta bukaci Ganin Taliban Ta Shiga Cikin Tattaunawar Sulhu
Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Lavrov ne ya bayyana haka a wani taro da aka yi a birnin Geneva yana maicewa: Wajibi ne ga gwamnatin kasar Afghanistan da ta zauna teburin tattaunawa da dukkanin bangarorin kasar, da su ka hada da Taliban
Ministan harkokin wajen kasar ta Rasha ya kuma ci gaba da cewa; Muna cikin damuwa akan yadda al'amurran kasar Afghanistan ke kara tabarbarewa, don haka tattaunawa ce kadai hanyar maganin rikicin
Rasha ta shirya gudanar da taron sulhu na Afghanistan a birnin Moscow wanda zai sami halartar kasashen Iran, Afghanista, China, Pakistan da sauran kasashe Asiya ta tskiya
A jiya Laraba ma babban magatakardar Majalisar Dinkin Duniya Antonio Gutress ya ce; A yanzu ya zama wajibi fiye da kowane lokaci a samo hanyar da za a warware matsalar rikicin kasar Afghanistan
A nashi gefen shugaban kasar Afghanistan Muhammad Ashraf Ghani ya ce; Kasar tana son ganin sulhu ya tabbata wanda zai kunshi kungiyar Taliban.
Taron na Geneva na kwanaki biyu ya sami halartar manyan baki da su ka fito daga kasashe 60 na duniya wanda MaJalisar Dinkin Duniya ta dauki nauyin gudanar da shi