G20 : Ganawar Trump Da Putin Na Nan Daram_Kremlin
Nov 29, 2018 10:15 UTC
Fadar shugaban kasa a Rasha ta tabbatar da cewa za'a yi ganawa tsakanin shugaban kasar Vladimir Putin da takwaransa na Amurka Donald a daura da taron G20 da za'a yi a Argentina.
Da yake sanar da hakan kakakin fadar shugaban kasar ta Rasha, Dmitri Peskov, ya ce Ita ma dai gwamnatin Washigton ta tabbatar da ganawar wacce za'ayi a ranar Asabar 1 ga watan Disamba.
Daga cikin batutuwan da shuwagabannin zasu tattauna har da batun alakar dake tsakaninsu, tsaro, da dai wasu batutuwa da suka shafi halin da ake ciki a wasu sassan duniya.
Tunda farko dai an yi ta yayata cewa Amurka ta soke ganawar shugawabannin biyu, saboda rikicin da ya kunno kai tsakanin kasashen Rasha da Ukreine.
Tags