Hizbullah Ta Ja Kunnen 'Isra'ila' Kan Kawo Hari Kasar Labanon
Kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ta ja kunnen haramtacciyar kasar Isra'ila da cewa duk wani wuce gona da iri da za ta yi kan kasar Labanon to kuwa ba zai tafi haka kawai ba tare da martani mai kaushi daga wajen kungiyar ba.
Rahotanni daga kasar Labanon din sun jiyo Hasan Hoballah, daya daga cikin membobin majalisar siyasa ta kungiyar ta Hizbullah yana fadin hakan inda ya ce: Lokacin da 'Isra'ila' za ta kawo hari Labanon ta sha ya wuce. A halin yanzu dai duk lokacin da Isra'ila ta kawo hari Labanon to kuwa za ta fuskanci gagarumin mai da martani daga wajen dakarun Hizbullah din.
Hoballah ya kara da cewa a halin yanzu dai dakarun kungiyar ta Hizbullah suna cikin dukkanin shirin da ya kamata a ce suna da shi wajen mayar da martani ga Isra'ilan, kamar yadda ya ce dakarun suna ci gaba da sanya ido kan abubuwan da ke faruwa.
Kalamin na jami'in Hizbullah din ya zo bayan da sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila sun sanar da fara wani shiri da suka kira kokarin rusa ramukan karkashin kasa da Hizbullah suka tona akan iyakokin Lebanon da Palastine da aka mamaye.