Faransa Ta Bukaci Trump Ya Shiga Tafiye Tafiyensa
https://parstoday.ir/ha/news/world-i34385-faransa_ta_bukaci_trump_ya_shiga_tafiye_tafiyensa
Mahukuntan Paris, sun bukaci shugaban Amurka Donald Trump, da ya shiga tafiye tafiyensa, ya daina tsoma baki a cikin harkokin cikin gida na kasar.
(last modified 2018-12-09T15:55:32+00:00 )
Dec 09, 2018 15:55 UTC
  • Faransa Ta Bukaci Trump Ya Shiga Tafiye Tafiyensa

Mahukuntan Paris, sun bukaci shugaban Amurka Donald Trump, da ya shiga tafiye tafiyensa, ya daina tsoma baki a cikin harkokin cikin gida na kasar.

Da yake bayyana hakan a wata muhawara a gidan radiyo t ahadin gwiwa RTL /Le Figaro/LCI, ministan harkokin wajen kasar ta Faransa, Jean-Yves Le Drian, ya bukaci Trump, da ya daina tsoma baki a cikin harkokin siyasar cikin gida ta kasar.

Mista le Drien, ya ce ya gaya wa Trump kuma shugaban kasar ma Emmanuel Macron ya fada masa cewa, basa shishigi a harkokin cikin gidan Amurka, don haka a daina su ma tsoma masu baki a harkokin kasa..

Wannan dai na zuwa ne bayan da shugaba Trump na Amurka ya wallafa a shaffinsa na Twitter, cewa '' abun damuwa ne halin da Faransa ke ciki a daidai lokacin da 'yan kasar ke bore kan tsadar rayuwa a jiya Asabar, sannan kuma ya bukaci a kawo karshen yarjejeniyar yanayin da aka cimma a Paris a 2015.