Dan Bindiga Ya Hallaka Mutum AKalla 4 A Faransa
Rahotanni daga Faransa na cewa mutane a kalla hudu ne suka mutu a yayin wata musayar wuta a tsakiyar birnin Strasburg da yammacin jiya Talata.
A yanzu haka dai an ayyana shirin ko ta kwana a fadin kasar, biyo lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum uku da raunata wasu 12, da suka hada da guda shida dake cikin mawuyacin hali a cewar ministan cikin gida na kasar Christophe Castaner.
Bayanai daga kasar sun ce an karfafa kwararen matakai na jami'an tsaro a birnin da iyakokinsa, a yayin da kuma 'yan sanda ke ci gaba da farautar maharbin.
Tuni dai aka tantance maharbin mai shekaru 29, wanda kuma aka bayyana shi a matsayin sanane kasancewar ya taba yin kaso saboda wasu ayyukansa da halaye da suka hada rikici da kuma nacewa kan addini.
A game da hakan dai sashen yaki da ta'addanci na kasar ya ce yana da kwararen hujjoji domin bude bincike kan kisa da yunkurin kisa mai nasaba da kungiyoyin 'yan ta'adda.