Faransa : 'Yan Sanda Sun Bindige Maharin Strasbourg
Rahotanni daga Faransa na cewa 'yan sanda a kasar sun harbe, Cherif Chekatt, dan bindigan nan da ya kashe mutune uku da raunata wasu 13 a birnin Strasbourg a ranar Talata data gabata.
Bayanai sun nuna cewa an harbe dan bindigan har lahira, da yammacin jiya Alhamis a anguwar Neudorf dake kudancin birnin na Strasbourg dake gabashin faransa a iayaka da Jamus.
Ministan cikin gida na kasar Christophe Castaner, ya ce 'yan sanda sun gano maharbin ne a lokacin da yake yawo kan tituna sukayi kokarin cafke shi, amma ya yi kokarin harbinsu, nan ne 'yan sanda suka maida masa martani suka kuma bindige shi.
Bayan sanar da mutuwarsa, kungiyar 'yan ta'adda ta (IS), ta fitar da wata sanarwa dake cewa maharbin Cherif Chekatt, wani mayakinta ne.
A wani sako da ya aike a shafinsa na Twitter, shugaban kasar ta Faransa, Emanuell Macron ya godewa daukacin jami'an tsaron kasarsa, tare da shan alwashin ci gaba da yaki da ta'addanci.