Rasha Ta Yi Maraba Da Fitar Sojojin Amurka Daga Siriya
Shugaban kasar Rasha Viladimin Putin ya yi maraba da matakin da shugaba Trmp na Amurka ya dauka da fitar da sojojin kasarsa daga kasar Siriya
A yayin wani taron manema labarai da suka kira a daren jiya laraba, tsakanin Shugaba Viladimin Putin na kasar Rasha da Rajab Tayyib Ordugan na Kasar Turkiya a Birnin Moscw, Shugaba Putin ya ce: matakin da kasar Amurka ta dauka na kwashe sojojin kasar daga Siriya, zai rage radadin rashin tsaro a kasar Siriya.
Shugaba Putin ya kara da cewa goyon bayan kawo karshen ayyukan Soja a Siriya bai kamata ya yi tasiri da fada da ta'addanci ba.
Yayin da yake nuna goyon bayansa kan matakin Amurka na kwashe sojojinta daga arewacin kasar Siriya, Shugaba Putin ya bukaci gwamnatin Siriya da ta fara tattaunawa kurdawan kasar.
A nasa bangare, Shugaba Rajab Tayyib Ordugan ya ce bangarorin biyu sun tattauna kan matakin da hukumomin Amurka suka dauka na kwashe sojojin su daga kasar Siriya.
A yayin da yake ishara kan ci gaba da tattaunawa na samar da wani yankin tsaro a arewacin Siriya kusa da iyaka da kasarsa, Ordugan ya bayyana cewa manufar Turkiya shi ne yaki da kungiyoyin 'yan ta'adda a Siriya.
har ila yau shugaban kasar Turkiyan ya tabbatar da cewa alaka tsakanin buranan Ankara da Moscow ta ci gaba, kuma a bangaren kasuwanci kasashen biyu sun yi mu'amala da ta kai ta dala billiyon 26 a shekarar 2018 din da ta gabata.