An Kama Masu Zanga-Zanga 29 A Faransa
Hukumar 'yansanda ta kasar Faransa ta bada sanarwan cewa jami'an hukumar sun kama mutane 29 a jiya Asabar, wato karo na 14 kenan da mutanen kasar suke zanga-zangar kin jinin tsarin jari hujja a kasar.
Tashar talabijin ta BFMTV ta nakalto jami'an gwamnatin kasar ta Faransa sunan fadar haka a yau Lahadi, sun kuma kara da cewa mutane 41,400 ne suka shiga zanga-zanga ta mako 14 na nuna rashin amincewa da tsarin jari hujja a kasar.

Labarin ya kara da cewa tun lokacinda aka fara zanga-zanfar a karshen shekarar da ta gabata jami'an 'yansandan kasar 1,300 ne suka ji rauni.
Tun cikin tsakiyar watan Nuwamban shekarar da ta gabata ce masu adawa da tsarin jarin hujju a kasar Faransa suka fara zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da karan farashin makamashi da kuma haraji wanda gwamnatin shugaban Emmanuel Macron ya yi.
Amma duk da cewa gwamnatin kasar ta janye harajin amma masu adawa da tsarin jari hujja sun ci gaba da zanga-zanga a ko wace ranar Asabar don ganin bayan gwamantin shugaban Emmanuel Macron.