Gurbataciyar Giya Ta Hallaka Mutum 69 A India
(last modified Sat, 23 Feb 2019 15:37:12 GMT )
Feb 23, 2019 15:37 UTC
  • Gurbataciyar Giya Ta Hallaka Mutum 69 A India

A kasar India, mutum 69 ne aka tabbatar sun bakunci lahira, sakamakon kwankwadar gurbataciyar giya a lardin Golaghat dake yankin Assam a arewa maso gabashin kasar.

Ko baya ga wadanda suka hallaka, akwai wasu kimanin 200 da suke kwance a asibiti bayan da suka sha gurbataciyar giyar.

Bayanai sun nuna cewa mafi yawa daga cikin wadanda lamarin ya rusa dasu, mata ne ma'aikata a gonnakin ganyen shahi a yankin.

Wani likita a asibitin yankin, ya shaidawa kamfanin dilancin labaren AFP cewa, mutanen da ake kawowa a asibitin na fama matsalar nunfashi da amai da kuma mugun ciwon kirji.

Rahotanni sun nuna cewa wanann ba shi ne karo na farko ba da irin hakan take faruwa, inda ko a makwanni biyu da suka gabata ma daruruwan mutane suka sheka lahira a cikin irin wannan lamari.

Tuni dai gwamnan yankin na Assam, ya bada umarnin gudanar da bincike kan lamarin, a yayinda wasu rahotanni ke cewa tuni 'yan sanda suka cafke wani mutum dake saida barasa a yankin, tare kuma da korar wasu ma'aikatan haraji biyu, saboda rashin daukar matakai kafin shigar da giyar a kasuwa.