Trump Ya Nada Kelly Knight, Sabuwar Jekadiyar Amurka A MDD
Shugaba Donald Trump, na Amurka ya nada jami'ar diflomatsiyar kasar, Kelly Knight Craft, a matsayin sabuwar jekadiyar kasar a MDD.
Trump, ya nada Kelly Knight Craft ne domin maye gurbin, Nikki Haley, wacce ta sanar da murabus na ba zata daga mukamin aaaaaa watannin da suka gabata.
Kelly Knight, dai ita ce yanzu haka jekadiyar Amurka a kasar Canada.
Shugaba Trump ya sanar da nada Kelly ne a shafinsa na twitter, inda yake cewa, jami'ar tayi aiki mai matukar kyau wajen wakiltar kasarmu, a don haka bana shakku kuma akan zamanta wakiliyar kasarmu akan wannan babban mukamin, a don haka yake mai taya murna da ita da iyallanta.
Haka ma jami'ar ta samu sakon taya murna daga sakataren harkokin wajen Amurka, Mike Pompeo.
Wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen Amurka, ta fitar ta ce, jami'ar Craft, ta kare tsaron kasar da kuma tattalin kasar a Canada, kuma tana da kwarewar da zata yin hakan a MDD.
Saidai duk da hakan ana bukatar majalisar dattijan kasar ta Amurka ta amince da nadin da akayi mata.